KARYA TAMBAYA/ ابطال السحر صحيح - JAWAHIRUL AZKAR

Breaking

Post Top Ad

Monday, September 16, 2019

KARYA TAMBAYA/ ابطال السحر صحيح

Assalamu alaikum Wa Rahmatullah jama'a masu Bibiyar wannan shafi Na jawahirul azkar, Ganin yadda yawancin jama'a ke bina ta inbox, suna Neman Dafa'i  Da kuma Ibdalil sihri, Naga ya kamata Narubuta shi anan ta yadda Za a amfana dashi ako da yaushe.
Wannan Sirri Yana da mutukar amfani wajen lalata dukkan wani sihri da jifa wanda aka yi akan wani Ko wata musamman don lalata harkokin mutum Ko korarwa mace samari kuma ahanata Aure Na tsawon shekaru (Wa iyazubillah)  Ko kuma wata Rashin lafiya da taki ci, taki cinye wa.
Abu Na farko dai Sai Anemi kaikayi koma kan mashekiya sannan arubuta wannan Hatimin Tare Da waɗan nan ayoyin Masu zuwa ajikin Allo sannan awanke da Ruwa kaɗan, Sannan azuba Garin maganin ( Kaikayi koma kan mashekiya) cikin rubutun ya tsotse Ruwan sannan abarshi ya bushe a rana, za a fara Turaren Hayaki dashi kwana 3 zuwa 7. Insha Allah Duk wani sihri da kullin da yake jikin mutum Sai warware cikin gaggawa. Kuma harkokin kasuwanci Za su buɗe. Ga Hatimin
كلياش كلوش يبطوش ياشا طليش اطارش كا رش فيروش غيوش كياش

الله لا إله إلا هو الحي القيوم لا تأخذه سنة ولا نوم له ما في السموات وما في الأرض من ذا الذي يشفع عنده إلا بإذنه يعلم ما ما بين أيديهم وما خلفهم ولا يحيطون بشئ من علمه إلا بما شاء وسع كرسيه السموات والأرض ولايعوده حفظها و هو العلي العظيم وألقي السحرة سا جدين قال موسي ما جئتم به السحر إن الله سيبطله إن الله لا يصلح عمل المفسدين. ويحق الله الحق بكلماته ولو كره المجرمون
Rubutun Qafa 3 Hatimin kuma Qafa 1 tak.

Allah Ya biya mana Dukkan buƙatun mu.

3 comments: