TASARRAFIN FATIHA DON NEMAN BIYAN BUƘATA - JAWAHIRUL AZKAR

Breaking

Post Top Ad

Thursday, October 17, 2019

TASARRAFIN FATIHA DON NEMAN BIYAN BUƘATA

Assalamu alaikum Wa Rahmatullah.
Wannan Sirri Da Zanyi Bayanin Shi yanzu Tasarrafin FATIHA ne, kuma sahiyhan Mujarrabun. Kuma ana amfani da shi akan kowacce irin Buƙata Musamman idan Mutum ya shiga cikin Wani Hali Na Rashin Kuɗi Ko Tsayawar Harka, Ko kuma Ya kasance mutum yana cikin Tsananin Bashi sannan baida Abin Biya. To Bi Iznil Lahi Zai sami biyan Bukata cikin Gaggawa. Sannan kuma Akan kowane buƙata idan aka yi wannan aiki To babu shakka Sai an sami Ni'imar Rayuwa Da walwala Tare Da Kwanciyar hankali a Tsawon Wata Guda.( Wannan aiki Gwadajje ne). Saboda haka Ranar Lahadi ake so a Fara wannan aiki.
1. LAHADI:- الحمد لله رب العالمين ١٠٠٠
يا وهاب هبلي ١٠٠
2. LITININ:- الرحمن الرحيم (١٠٠٠
   يا رزاق أرزقني ١٠٠
3. TALATA:- ملك يوم الدين ١٠٠٠
  يا فتاح افتحلي أبواب الخير ١٠٠
4. LARABA:- اياك نعبد واياك نستعين ١٠٠٠
   يا معطي أعطيني ١٠٠
5. ALKAMIS:- اهدنا الصراط المستقيم ١٠٠٠
   يا واسع أو سعني ١٠٠
6. JUMA'A:- صراط الذين أنعمت عليهم ١٠٠٠
   يا مغني اغنني١٠٠
ASABAR:- غير المغضوب عليهم ولا الضالين ١٠٠٠
  يا راشد أرشدوني ١٠٠
Idan an kammala aikin sai ayi Sadaka da abin da ya sauwaƙa Kamar Waina Da sugar ko Kosai da yaji idan kuma akwai wadata Sai a yanka Zakara abaiwa yara Sadaka. Ga Hatimin
Wanda za a Rubuta asa agaba ayi Tawassali dashi lokacin yin aikin
Ga kuma Huɗubar Da za a karanta Qafa 3 kullum bayan an kammala aikin


HUƊUBA:-

ALLAHUMMA YA MUFTAHUL ABWABI WAYA MUSABBIBAL ASBAB WAYA MUQALLIBAL QULUBI WAL ABSAR WAYA DALIYLAL MUTAHAIYIRIYNA WAYA GIYASAL MUSTAGISIYNA WAYA MUKHRIJAL MAHZUWNIYNA AGSINIY . TAWAKKALTU ALAIKA YA RABBI QADHAITA FARADHIYTU FAWA DHATU AMRIY ILAIKA YA RAZAQU YA FATAHU YA BASIƊU WA SALLALLAHU ALA KHAIRI KALQIHI MUHAMMAD WA AHLIHI WA SAHABIHI AJMA'IN.

1 comment:

  1. Allah Ya saka da alkhairi,
    Za a iya rataya hatimin a tasbaha ko dole sai dai a rubuta a kasa?

    ReplyDelete