Asraru Rauhaniyya - JAWAHIRUL AZKAR

Breaking

Post Top Ad

Saturday, February 8, 2020

Asraru Rauhaniyya


 


Ismillahil Aziym

Assalamu alaikum wa rahmatullah, Yau dai nayi niyya kuma na Nishaɗantu da kawo wani Babban ismiy wanda ake iya tasrifi dashi ta hanyoyi masu yawa.kuma Yana da fa'idodi har guda Arba'in da Biyar (45). Waɗanda suka haɗa da Asrarul Rauhaniyya da kuma Wasu daga cikin buƙatummu na Yau da kullum.
Shi dai wannan sirri bashi da wuyar aikatawa kuma "Wallahi tallafi" duk buƙatar da aka sa agaba cikin Iklasi Sai an samu biyan buƙatar cikin gaggawa. Kuma shi wannan sirrin ako wacce rana ana iya aikata shi. Join the fastest Growing Airdrop In History With Over 2 Million singups In 28 Days
  • 1.Kashful qulub:- Wanda yake so Allah ya saka masa ilhama a cikin zuciya ko kuma ariƙa nuna masa duk abinda yake buƙata cikin Barci, Sai ya riƙa karanta wannan sirrin Qafa 3 Bayan sallar Asuba, Sannan kuma Qafa 5 bayan sallar la'asar.
  • 2. MUHIBBA;- Domin haɗa soyayya tsakanin miji da mata Ko saurayi da budurwa za a karanta wannan sirrin Qafa 9 cikin dare tsawon kwana 3 ayi turaran hayaƙi da Kanamfari .
  • 3. IBƊALIL SIHR;- Wanda ake Tunanin an yi masa sihri ko kuma Matsalar jinnu Ko matar da jini yaƙi dauke mata za a rubuta masu wanann sirrin Qafa 1 har kwana 7 asha zai warke bi iznil Lahi.
  • 4. Don Neman samun Ɗaukaka da yalwatar Arziki za a riƙa karanta wannan sirrin Qafa 45.
  • 5. Domin kafin Gida daga sharrin Ɓarayi Ko mafasa sai a rubuta wannan sirrin Qafa 1 cikin farar takarda a rataye Ko a binne a wurin.
  • 6. Don Neman kariya daga mafasa da Ɓarayin hanya wajen tafiye-tafiye za a karanta wannan sirrin Qafa 9 kafin a yi tafiyar.
  • 7. Mallake Mace Ko Namiji ta yadda baza ta iya yin hakurin Rashin ganin ka Ko jin maganar ka Na sa'a 1 ba. Sai a karanta wannan Addu'ar Qafa 45 Ranar Lahadi ayi turaran hayaƙi da Kanamfari.
  •  
  •  
  • 8. Tamlikul Jinnu wal Arwahu:- Wanda yake neman mallakar RAUHANAI farare zai fara karanta wannan sirrin Ranar Lahadi ta farkon wata Qafa 45 kullum har tsawon kwanaki ashirin da daya (21) Kafin ya gama zai ga abin mamaki wanda babu tsoratarwa kuma lokacin zasu fara maka biyayya da kuma Hidima. Bayan an mallaki waɗannan halittu daga wannan Lokacin Qafa 3 kacal za a karanta sirrin sannan a basu umarnin da ake bukata.

1 comment: