SU WAYE RAUHANAI?
A matsayi na na Dalibin ilimi mai bincike kan abinda ya shafi iliman Taurari (Ramli/hisabi/falaki da sirruka ) lallai, Ba shakka na dan ji malamai na na ta bayani akan wannan maudu'i kuma na dan fahimci wasu abubuwa kadan shine zanyi karambani wajen bada ɗan qaramin bayani bakin iyawa ta kasancewar wasu mutane suna iqirarin cewa suna aiki da Rauhanai inda suke taimaka musu wajen bada magani ko wasu ayyukansu na rayuwa. To su waye Rauhanai kuma aiki da su ya halarta ? Sannan kuma yaya Ka'idar aiki da su yake?
Da farko dai kalmar (Rauhani) tana nufin wani boyayyen ilimi wanda Allah Ya kebanci wasu daga cikin bayinsa da shi, in ba su ba,ba wanda ya sanshi. Allah ne yake zabar wasu daga cikin bayinsa Ya sanar da su.
Kenan kalmar "Rauhaniy" tana nufin wanda yake da ilimin da kowa bai sani ba sai shi
To amma su waye Rauhanan da wasu Malamai ko Shehunai da sauran wasu mutane suke ikirarin suna aiki da su?
Malaman da suka kawo maganar Rauhaniy a littattafan ɗibbu daban-daban hakika sunyi sabani akana asalin Rauhaniy da kuma menene shi. Maganganu mafiya shahara dai su ne guda uku.
*Magana ta farko :- ita ce Su Rauhanay Mala'iku ne. Allah Ya halicce su ne kamar sauran Mala'iku, saidai su suna mu'amala da mutane. Tsarkin zuciyar mutum da kuma kula da ibada shi yake sawa wadannan Mala'iku su kusance shi har su dinga mu'amala da shi.
Kowane mutum yana da Aljani kuma yana da Mala'ika a tare da shi. Idan aikin sabonka yayi yawa to Aljaninka shine zai tasiri akanka. idan kuma aikin ibadarka ya rinjaya to Mala'ikanka zai zama shi ne jagoranka. Wannan Mala'ikan mai maka jagora shine Rauhaninka.
Ya danganta da yadda ya yaba da hankalinka da nutsuwarka, sai ya bayyana maka kansa a fili kuma ya dinga zuwa kuna mu'amala, yana taimaka maka akan wasu ayyukanka na rayuwa da ibada.
Kowane mutum yana da wannan Mala'ika Rauhaniyyi a tare da shi, kuma sunanka yana kama da sunan Rauhaninka. Misali idan sunanka Bashir* to sunan Rauhaninka (Bashiru'iylu)ko kuma Idan sunanka Musa* to sunan Rauhaninka Musa'iylu*. Ma'ana kalmar (iylu) ake karawa a gaban sunan mutum shikenan sunan Rauhaninsa ya fita.
Wannan ita ce magana ta farko.
Ka'idodin Aiki Da Rauhanai.
1. Mutum ya kasance mai yawan yin Ibada, Tare da yin sallolin Dare (Kiyamul Laili).
2. Mutum ya kasance mai yawan yin Azumin Nafila.
3. Mutum ya kasance Baya kwana da Janaba ajikinsa.
4. Tarkul ma'asiy:- Nisantar barna *** Ta bangaren mata***
5. Cin Halak da yawan yin Azkar
6. Yawan yin amfani da Turare mai kamshi ajikinka da kuma Dakinka.
Matukar mutum ya riƙe wannan ka'idodi to babu makawa Idan yaja QASMIN Burhatiya Ko Jaljalutiya Ko kuma wani Ismin kiran Rauhaniy/Ko Aljanu, To Lalle Zasu Halarta cikin gaggawa, Har ma ya gansu da idonsa.
Allah yasaka da alkhairi Malam,
ReplyDeleteMalam yaushe Za afara fatawa akan Ramli?
Ko Shima yanada shafinsa ne na Musamman?
Allah ya biya bukatan Malam
Allah yasaka kuma yajikan tsofaffi, amin.
Ina mai sanar maka da cewa Nan da wani ɗan lokaci kaɗan Zan fara rubutu akan ilmin Ramli da kuma Hisabi
DeleteMalam, wallahi ka wa yar mun da kai akan wadannan halittu (Rauhanai).
ReplyDeleteAllah yabiyaka da dukkan alkhairinsa.
Ameen Alfarmar Nabiyul Rahmati
Deleteشكراًجزاك اللهُ خيرًا
ReplyDeleteAllah ya saka da alheri
ReplyDeletemasha Allah, Allah saka da alheri
ReplyDelete