- 1. Abu na farko dai Yin Azumin Kwana 3 acikin Halwa. Kuma Ƙa'idar Azumin shine Babu cin Nama Ko Kifi Ko Kwai Ko Nono Ko kuma Zuma, Dukkan wani abinci da ya fito daga jikin ( Abu Mai Rai) Haka kuma Ka Nisanci Yin Mu'amala da Albasa da kuma Tafarnuwa A ranakun da kake aikin.
- 2. Ka kasance Cikin Tsarkin Jiki da Kuma Zuciya. Tufafi Masu Tsarki da kuma Wurin Aiki Shima ya zama Mai Qamshi da Turare.
- 3. TURARAN AIKIN SUNE:-
- a. Sandal Ahmar
- b. Sandarus
- c. Uwdi
- d. Lubban Zakar.
- YADDA AKE YIN AIKIN SHINE:-
- Za a Karanta ( Inna A'aɗaina Kal Khausar) Har zuwa Karshen Surah Qafa ( 1000). Duk Bayan Sallar Farillah. Wato a kullum sallah Biyar Ya zama jimilla (5000) kenan a kullum.
- To bayan kowacce sallah idan an gama Wuridin sai ka karanta wannan Addu'ar Qafa (1).
- اللهم اني اسألك بموجبات رحمتك وعزأيم مغفرتك أن تسخرلي خادم هذه السورة السيد عبد الكريم إلا ما أجبت وسمعت وأطعمت شرديخ2 مرديخ2 بمن كلم موسي تكليما علي جبل طور سينا الواحا2 العجل 2 الساعة 2 بارك الله فيكم و عليكم.
- Bayan Kammala Aikin Na kwana 3. Cikin daren Zai zo maka SAYYADI ABDUL KAREEM kuma ya Tambaye ka ka, cewa me kake so?
- Sai ka amsa masa da cewa" Ina so kayi mini alƙawarin Taimakona A Duk Lokacin da Nake Da Buƙata "
- Idan Har kuka ƙulla alƙawarin sai ka umarce shi da ya Rubuta maka Ɗalasami Ko Hatimin idan ya baka To Alhamdulillah. Duk Lokacin da kake da wata Buƙata sai ka karanta surar Qafa (1) sannan kace" YA ABDUL KAREEM"
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Yau Kuma Insha Allahu Zanyi Bayani akan yadda za a gabatar da wannan aiki dalla-dalla. Yadda za a mallaki Rauhanin (Suratul Khausar) Wato " Inna A'aɗaina Kal Khausar"
No comments:
Post a Comment