SAYYADI KANDA YASU KHADIMIN AYATUL KURSIYYU - JAWAHIRUL AZKAR

Breaking

Post Top Ad

Thursday, January 2, 2020

SAYYADI KANDA YASU KHADIMIN AYATUL KURSIYYU

Assalamu alaikum wa rahmatullah, Yau Kuma Insha Allahu Darasin namu akan Rauhanin da ke Kan (AYATUL KURSIYYU) ne, Zanyi Bayani yadda ake gudanar da aikin Don samun Nasara tare da Dukkan wani biyan buƙata

MENE NE RAUHANAI?
⁉️💢⁉️⁉️‼️⁉️‼️⁉️

Rauhanai wasu Rundunar Halittun Allah ne wanda aka haliccesu Domin yin Hidima ga ayoyin Alkur'ani sunan Allah da Wasu Harufai

Kowacce aya ta cikin Alku'ani tana da Rauhanai  wayanda Allah ya haliccesu saboda ita hakama kowanne Daya daga cikin sunayen Allah yana da Rauhani wanda yake yiwa wannan sunan Hidima

Hakama kowacce sura ta cikin Alku'ani tana da Rauhanai wayanda sukeyi mata hidima  ,malaman musulunci sun karawa juna Sani game da jinsin Raunahai shin Aljanune ko kuma mala'iku ??

Mafi Rinjaye daga cikin malamai sun hadu akan cewa Rauhanai Rundunar mala'ikune wanda Allah ya halicce su domin yiwa ayoyin Allah da sunayensa Hidima.


sannan wasu daga cikin Manyan malamai  kuma sun tafi akan cewa musulmai daga cikin Aljanu sune ake kira Rauhanai , Kuma 🌞 kowa Ya  dalilinsa akan hakan. To irin waɗannan sune masu Taimako kuma basa cutarwa tunda masu tsarki ne, Kuma suna son Mutane masu Tsarkin Jiki da Tsarkin Ruhi.

  • Amma Duk da haka wannan aikin yana da sharuɗa har Goma sha uku. Gasu zan kawo su ɗaya bayan ɗaya.
  • 1. Alwala
  • 2. Tsarkin Wurin Da za a yi aikin
  • 3. Zuba Turare Mai Kamshi Na ruwa Ko Na hayaƙi.
  • 4. Gabatar da Yin nafilfili Ko Raka'a biyu ce, Ya wadatar
  • 5. Karanta Addu'ar Neman Tsari daga dukkan Wani Abin cutarwa.
  • 6. Sarful A'amar ( koran duk wani shaiɗanin Aljani daga wurin)
  •    7. Karanta dadin ayar ( AYATUL KURSIYYU) 313 daidai Ba ragi ba ƙari 8.  Fuskantar Alqiblah (Gabas)
  • 9.  Kashe Fitila Ko Lantarki lokacin aikin
  • 10. Nutsuwa tare da barin waswasi
  • Rufe idanu lokacin Yin aikin har sai an kammala Adadin ayar.
  • 11. Mayar da Gaisuwa ga Rauhanin Lokacin da yayi maka magana.
  • 12. Sarrafa Rauhanin Lokacin da ka gama Ganawa da shi.
  • GA TAHSIN SAHIHUN ( Addu'ar Neman Kariya Daga Dukkan Wani Abin Cutarwa (Aljani ko Mugun mutum).
  •  بسم الله الرحمن الرحيم
  • لااله إلا الله بيتي وبين أعدأءي لااله الاالله بيني وبين خصمأءي جبلا حاءلا و سد ما نعا وسترا محجوبا و سيفا قاطعا و نار محرقة و بحرا عميقا لا يصلون إلي لابقول ولا بفعل ولا بسوء من يوم
  • إلي غد من الي أبد فسيكفيكهم الله هوالسميع العليم
  • ولا حول ولا قوة إلا باالله العلي العظيم
  • اللهم إن جاءوني فردهم و إن جاروأ علي فعهدهم فانك أنت الله ربي و ربهم و رب الخلاءق كلهم.
  • Wannan itace Babbar addu'a ta Neman Tsari daga dukkan bangarori Na Aljani da kuma Bil Adamiyya.
GA KUMA ISRAFIL AMAR IRIN WANDA ZA A KARANTA:-

1. INNA ANZAL NAHU FIY LAIKATUL QADR Qafa 3. (Amma idan akazo wurin " salamun hiya" za a maimata har sau 3. 
Misali:- ( salamun hiya salamun hiya salamun hiya) sannan aci gaba da karanta wannan Addu'ar
انصرفوا يا عمار هذا المكان من هذاالمحل حتي أقضي حاجتي ثم يعودون إلي مكانكم باركالله فيكم وعليكم sannan kuma ka karantaISRAFIL AMAR Daga nan sai ka fara Wuridin Ayatullah KURSIYYU 313  Duk Ɗari ka faɗi wannan Addu'ar Qafa 3
اللهم اني اسالك بحق اية الكرسي عندك وشرفها لديك أن تقضي حاجتي (....) وصل الله علي سيدنا محمد وعلي اله وسلم
Haƙiƙa Na yarda da wannan aikin saboda za ka ji maganar Sayyidi ta bangon Ɗakinka a lokacin da zai yi maka sallama kafin ya bayyana, kuma matukar akwai tsoro a zuciyarka bazai bayyana ba Sai dai ka riqa jin maganar sa ba tare da ka ganshi ba.

TURARAN AIKIN SUNE;- 
1. Lubban Zakar
2. Jawiy
3. Kusbura
  

3 comments:

  1. Asl mlm Allah y kara basira y ake amfani da
    lubban zakar
    jawiy
    kubura
    ya zan amfani dasu ngde

    ReplyDelete
  2. Malam Mubarak Turaran hayaƙi ake yi dasu

    ReplyDelete
  3. Assalamu alaikhum malam Allah kara ma daraja,don Allah malam inason arubutamun adu'oinnan da Harafin hausa saboda karatun ba wasali ya na ban wahala, sannan kuma mutun zai iya yin aikin da kowani lokashi neh?..... na gode

    ReplyDelete