ALIF LAMIM TAFRIDA BA A BUGUN KI SAI TA ƁACI
Assalamu alaikum wa rahmatullah, wannan sirrin yana da fa'idodi masu tarin yawa. Muhimmin abin da aka fi yi da (ALIF LAMIM TAFRIDA) shine Tasrifi, Bayan haka kuma sai Neman cimma buƙatar da ta gagara, kuma Ko wace iri ce, sai an samu biyan buƙatar. Rijiyoyi take dasu har guda goma sha ɗaya wanda komai na duniya yana Nan aciki, kuma Allah zai biya buƙatar da duk da ake so.
Samun matsayi a wurin aiki Ko Neman shugabancin siyasa Ko Neman Arziki duk ana yin amfani da ita. Siɗirarta shine:- " HAIQAƊAZU ƊAFAZA BAHAJA" kamar yadda zai zo a cikin takarda Nan Gaba, Sai a buga da bakwai, abinda ya fitar kuma daga ƙasa sai a jera " AHAMU SAQAKU HALWU YASU" Sannan a sa 4 ƙarƙashin shida a sake bugun cinye wa. Misali 4×6 = 24. Kunga ashirin da huɗu sun cinye kenan su zama sifili.
To, da haka za a gama cinye su har "ALIF" wato Allahu wahidul Qahhar yarage shi kaɗai. Amma Gaskiya yadda ake gudanar da aikin Ko wane sifili za a ajiye masa nashi sadakar wanda washegari da safe a je abaiwa mabuƙaci wanda ka sani. Sannan Turaran aikin sune:- Binta Sudan Kampani Ɗan Duwala.
Ana yin wannan aiki tsawon kwana 3 zuwa bakwai. Sannan kuma duk ɗaya daga cikin sunayen Allah da za a ja Wuridin, to Qafa 1111 ne Adadin sa. Sai Na ƙarshen Wato( ALIF) Shi kuma Wuridin sa ya kasu kashi biyu ne, Idan Neman wata Gagarumar biyan buƙata ce To Wuridin shine (Allahu Wahidul Qahhar) Idan kuma Tasrifi ne za a yi shi kuma Wuridin sa shine ( Allahu Wahidul Qahhar Allahu Ɗahfaluwshin) 313
Alf lamim tafrida/ jawahirul azkar |
Allah ya saka da Alkhairi AkramakaAllah
ReplyDeleteAfwan AkramakaAllah ina so a sake min bayani akan bugun cinye wa,ni lissafin gaba daya banga ne yadda akeyin sa ba Afwan AkramakaAllah ina so a Kara min haske akai.
ReplyDeleteBayan haka wuridin da mutum zai ja zai bar sunan Allah wanda ya fara da Alif a karshe ne ko kuma ko a farko ma zai iya farawa da shi.
ReplyDeleteAfwan AkramakaAllah ina so a min bayani akan kalma TASRIFI me ake nufi da ita.. Muna godiya Allah ya saka da Alkhairi
ReplyDeleteTasrifi Ana Nufin sarrafa ismiy ta Duk wata hanyar da mutum yake so, Alkhairi Ko sharri. Neman kuɗi Ko muƙami
Delete