DAFA'I DA JALABI - JAWAHIRUL AZKAR

Breaking

Post Top Ad

Wednesday, February 19, 2020

DAFA'I DA JALABI

    DAFA'I DA JALABI SAHIYHAN 

بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل علي سيدنا محمد النبي الامي و اله وسلمبسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى آله وصحبه وسلم

DAFA'I NE NA SAMMU(JIFA)  DA KUMA WARWARE MAKARU  ''SANNAN KUMA  JALABI NE MAI GIRMA''

Wato kariya daga sharrin maƙiya da jefe-jefen su. Da kuma samun Alkairi in Allah ya yarda

1. Zaka sami wata ciyawa da ake ce mata ƙaiƙayi koma kan masheƙiya. da Kainuwa sai ka rubuta INNA KAFAINAKAL MUSTAHAZI'UWN ƙafa dubu ɗaya da ɗari ɗaya da goma sha ɗaya 1111 sai SURATUL ƘURAISH أناكفينك مستهزعون LI'ILAFI. ƙafa ɗari uku da goma sha uku, 313 sai FALAƘI. DA NASI. kowacce ƙafa ɗari uku da goma sha Uku. (313)
Hatimin Dafa'i za a rubuta Qafa 1 a wanke

Sai a wanke asa acikin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya ɗin da Kainuwar. in ya bushe sai a dake sai a tan kaɗe.







Garin ana sha ne da NONO shikuma tsakin. ana sa baƙin algarif da baƙin kajiji da turaren luban zakar sai aƙara dakawa sannan sai asa turaren ALƘALIN GOMA a ciki. sannan sai a riƙa yin turare a jiki dashi wato hayaƙi Kenan.

IN ALLAH YA YARDA ZA'A SAMI KARIYA DAGA ALLAH DA WARWARE DUKKAN SIHIRI WATO JIFA NA MAƘIYA DA MAHASSADA.

2.  Ana samun ƙaiƙayi koma kan masheƙiya da Kainuwa da Sanya uwar magunguna. da Farar biya rana. da Farin gamo. da Farin Tsaf. da Shuwaka da Kafur. sai a haɗa su duka a dake sai asa man kaɗanya da turaren ALK'ALIN GOMA. da( BINTA SUDAN) da MISKI. sai a haɗa   su da baƙin sabulun salo. A cakuɗa ariƙa yin wanka.

DAFA'I NE DA JALABI. IN ALLAH YA YARDA BADAI SAMMU YA KAMA KABA IN KUMA ANMAKA ALLAH ZAI KARYASHI NAN TAKE DA IZININ ALLAH KUMA ƘOFOFIN ARZIƘI ZASU BUƊE DA IZININ ALLAH WANNAN SIRRIN MUJARRABI NE.
ALLAH YAYI MANA TSARI DA SHARRIN MASU SHARRI DA ƘULLIN MASU ƘULLI DA SIHIRIN MASU SIHIRI DA TSAFIN MASU TSAFI YA KUMA TSAREMU DA SHARRIN JUNNU DA MAYU DA MASU KAMBUN BAKA.

YA KUMA BUƊAWA KOWA ƘOFOFIN ARZIƘI DA NASARA DA DA CIGABA A RAYUWA YA KUMA BIYA MANA BUƘATUNMU NA ALKAIRI AMEEN.