SIRRIN YA WAHABU
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Yau Zanyi bayani akan sirrin" YA WAHABU" wanda yake babban sirri ne ga masu bugun Hisabi da kuma waɗanda ma basu iya bugun Hisabin ba, domin duk wanda ya shiga cikin wani mawuyacin Halin Rayuwa Ko kunci Na Fatara da Rashin Kuɗi Ko Abinci kuma yake so Allah ya fitar da shi daga wannan Fatarar to ya yi kokari ya aikata wannan sirrin, Babu shakka zai samu wadata cikin ƙanƙanin Lokaci yayi facaka da kuɗi kuma har ya taimaka wa wasu.
Mun sani cewa" YA WAHABU" tana da matakai na Adadi har guda biyar, to yanzu maganar da Zanyi akan manyan Adadin Guda biyu wato ( DOWKI TSAYE) Da Kuma ( FATAHTALIYA) .
Bugun Hisabin Ya WAHABU/ jawahirul azkar |
- DOWKI TSAYE:- Wannan ana yin Adadin" YA WAHABU HABLIY" Qafa 19264 kullum tsawon kwana 7 . A zamanin da malamai masu bugun Hisabi idan suna buƙatar su mallaki Doki to wannan shine sirrin da suke aikatawa kuma cikin ikon Allah washegari da safe za a yi musu sallama a kofar gida, suna lekowa sai dai su hangi Doki a tsaye wani Basarake Ko Attajiri ya aiko musu dashi. Kuma Doki a wancan lokacin Darajar su ɗaya da mota a Wannan zamanin da muke ciki.
- FATAHTALIYA:- Wannan shine mai Fatattakar Fatara. Shi kuma Adadin sa shine 134,848 . Za a yi sadaka da Waina da sugar lokacin da ake yin wannan sirrin, kuma Ana amfani da Turare mai ƙamshi wanda za a shafa a carbi da kuma tufafi .
-
No comments:
Post a Comment